logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bukaci kungiyar Kodagon kasar da ta janye batun yajin aikin gargadi

2023-09-05 09:19:09 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriyar ta yi kira ga kungiyar kodagon kasar NLC da ta dakatar da yunkurinta na tafiyar yajin aikin gargadi na kwanaki biyu.

Ministan kodago na kasar Simon Lalong ne ya bukaci hakan da yammacin jiya Litinin a birnin Abuja a wata ganawar da ya yi da shugabannin kungiyar Kodago ta TUC, ya ce yajin aikin zai iya yin illa matuka sannan kuma zai mayar da hannun agogo baya a kan nasarorin da gwamnati ta samu kawo yanzu.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Mrs Simon Lalong ya bukaci kungiyar ta NLC da ta kara baiwa gwamnati lokaci domin ta samu sukunin shawo kan matsalolin da ta gabatar mata, kasancewar dukkan bukatun kungiyar ba abu ne da za a iya nazarinsu a dan takaitaccen lokaci ba.

Ministan Kodagon ya ci gaba da bayanin cewa, “Gwamnatin tarayyar ta bayar da umarnin fitar da hatsi da kuma tan-tan na shinkafa domin rabawa ga masu karamin karfi,  kari a kan Naira biliyan 5 da aka rabawa kowacce jiha, ciki har da Abuja domin samar da karin kayan tallafi ga al’umma, har’ila yau shugaban kasa ya bayar da umarnin odar motocin bus masu amfani da makamashin CNG tare da umarnin aiwatar da manufar nan ta juya motoci da suke amfani da man fetur zuwa makamashin CNG a matsayin wata hanya ta rage tsadar makamashi a bangaren harkokin sufuri, nan kuma da ’yan wasu makonni, gwamnati za ta kara bullo da wasu matakai na rage radadi.”

A yau Talata ne kungiyar ta tsara gudanar da wannan yajin aiki wanda zai kare a gobe Laraba, ko da yake shugabannin kungiyar Kodago ta NLC sun kauracewa  taron na jiya da ministan ya gudanar. (Garba Abdullahi Bagwai)