logo

HAUSA

Tabarbarewar tsaro ya janyo rufe kasuwannin dabbobin guda 8 a jihar Zamfara

2023-09-04 10:30:36 CMG Hausa

 

Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da rufe wasu manyan kasuwanni 8 da ake hada-hadar cinikin dabbobi, biyo bayan ci gaba da tabarbarewar sha’anin tsaro a jihar.

Kwamishinan yada labaran jihar Alhaji Mannir Mu’azu Haidara ne ya sanar da hakan jiya Lahadi 3 ga wata cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai, inda ya ce, matakin na wucin gadi ne wanda kuma ya shafi kasuwannin dake kananan hukumomi 5 kawai.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Kananan hukumomin dai sun hada da Anka, Tsafe, Maru, Zurmi da kuma Bukkuyim wadanda su ne suke da manyan kasuwannin dabbobi a jihar ta Zamfara.

Ko da a ranar Juma’ar da ta gabata sai da gwamnan jihar ta Zamfara Alhaji Dauda Lawan ya fito fili ya koka ainun kan yadda al’amuran tsaro a jihar ke kara tabarbarewa.

A jawabin da ya gabatar yayin wani taron wa’azin addinin musulunci da ma’aikatar al’amuran addini ta jihar ta shirya a Gusau, fadar gwamnatin jihar, gwamna Dauda Lawan ya yi kira ga malaman addini da ’yan siyasar jihar da su hada kai wajen gudanar da addu’o’in dorewar zaman lafiya a jihar Zamfara.

“Lokacin da na amshi wannan mulki, na fahimci matsalolin dake fuskantar wannan jihar tamu, a ta ko’ina muna da matsaloli, yau dai tsaro ya addabi kowa. Yau mun wayi gari tafiya da rana ma tana kusan gagararmu, sannan yau idan muka yi la’akari da matsayinmu a Zamfara da yadda muke da imani da yadda muka sa addini a gabanmu, amma kuma yau Allah ya jarabce mu da masifu iri-iri. Yau muna cikin talauci, muna cikin ukubar tsaro, yunwa ta yi yawa, yaran mu ba sa iya zuwa makaranta, ba ka da lafiya ba za ka iya zuwa asibiti a ba ka magani ba.”

Daga tarayyar Najeriya, Garba Abdullahi Bagwai, CRI Hausa. (Garba Abdullahi Bagwai)