logo

HAUSA

Sojojin Sudan: wani harin da aka kai birnin Khartoum ya yi ajalin fararen hula 16

2023-09-04 10:29:12 CMG Hausa

Rundunar sojin Sudan ta sanar da cewa, wani harin da dakarun kai agajin gaggauwa ko (RSF) a takaice suka kai birnin Khartoum ranar Lahadi, ya halaka fararen hula 16.

Sojojin sun ce, mayakan RSF sun kai hare-haren wuce gona da iri kan yankunan Karari da Wad al-Bakhit dake arewacin Omdurman, arewa maso yammacin babban birnin kasar, inda suka kashe fararen hula 13 tare da jikkata wasu da dama.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta kara da cewa, mayakan sun kuma kai hari yankin Al-Maseed na kudancin Khartoum, inda suka bude wuta na kan mai uwa da wabi kan jama’a, lamarin da ya haddasa kisan fararen hula uku.

Sanarwar ta kara da cewa, an yi arangama tsakanin dakarun biyu a yankin Al-Shajara dake kudancin birnin Khartoum, wanda ya yi sanadin kashe mayakan RSF 5 tare da jikkata wasu 6.

Sai dai kuma, rundunar RSF, ta zargi sojojin Sudan da kai hare-hare kan wasu unguwannin dake Nyala, babban birnin jihar Darfur ta Kudu dake yammacin kasar, inda suka kashe fararen hula 14 tare da jikkata wasu da dama. (Ibrahim Yaya)