logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Sokoto za ta sayo motoci domin rabawa hukumomin tsaro a jihar

2023-09-03 16:16:27 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Sokoto dake arewacin Najeriya za ta kashe tsabar kudi sama da Naira biliyan daya wajen sayo motoci domin rabawa hukumomin tsaron dake jihar domin kara kaimi a aikin da suke yi na dakile karuwar aiyukan ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.

Gwamnatin ta yanke shawarar hakan ne yayin taron majalissar zartarwa ta jihar karo na farko da aka gudanar karkashin jagorancin gwamnan Jihar Alhaji Ahmed Aliyu Sokoto.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Yayin taron dai, majalissar zartarwa ta amince da sanya dokar ta baci a kan harkar abinci, inda karkashin wannan doka, gwamnati ta amince da kashe Naira biliyan 3.9 wajen sayo buhunan shinkafa dubu 57 da kuma buhun gyero dubu 26 domin rabawa ga al’ummar jihar kyauta.

Hon. Bashir Umarun Kwabo shi ne kwamishinan lura da harkokin bunkasar tattalin arziki da fasahar zamani, ya yi wa manema labarai karin bayani a kan kudaden da gwamnati ta ware domin sayo motocin aiki ga rukunan hukumomin tsaro dake jihar ta Sokoto.

“A zaman da aka yi na majalissar zartarwa a cimma matsaya a kan cewa za a sayo motoci guda 40, jami’an tsaro wadanda za su lakume kimanin Naira biliyan daya da miliyan 526 da Naira dubu 500, sai abu na biyu kuma, motoci guda 22 a kan kimanin kudaden Naira biliyan 1 da Naira miliyan 130 da kuma Naira dubu 470 kacal.”

Baya ga wadannan motoci da gwamnatin jihar ta amince a sayo, wani kamfanin siminti a jihar ta Sokoto kuma ya bayar da gudummawar motoci guda 10 domin dai rabawa ga kananan hukumomin jihar don tabbatar da kara ingantuwar harkokin tsaro a jihar baki daya. (Garba Abdullahi Bagwai)