logo

HAUSA

Shugaban kasar Najeriya ya kirawo jakadun Najeriya da ke kasashen waje su dawo gida

2023-09-03 17:01:55 CMG

A Jiya 2 ga wata ne shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya ba da umarni a kirawo jakadun Najeriya da ke a kasashen waje daga sassan duniya su koma gida.

A cewar wata sanarwa da fadar shugaban Najeriyar ta fitar a ranar 2 ga wata, Tinubu ya bayar da wannan umarni ne bayan ya yi nazari sosai kan halin da ofisoshin jakadancin Najeriya ke ciki.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, la'akari da cewa za a gudanar da babban taron Majalisar Dinkin Duniya a karshen wannan wata, zaunannun wakilan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya a New York da Geneva ba su cikin wannan kiran. (Yahaya)