logo

HAUSA

Shugaban Sudan ta kudu ya nada sabon ministan harkokin waje

2023-09-02 16:09:20 CMG Hausa

Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir, ya nada James Morgan Pitia, a matsayin sabon ministan harkokin waje da hadin gwiwa na kasar. Salva Kiir ya bayyana nadin mista Pitia ne a daren ranar Alhamis, cikin wani sako mai kunshe da umarnin shugaban kasa, wanda aka watsa ta gidan talabijin din kasa.

Kafin nadin sa, Pitia ya taba rike mukamin jakadan Sudan ta kudu a kasar Habasha, da kuma wakilin dindindin na kasar a kungiyar AU. Ya kuma maye gurbin tsohon ministan wajen kasar Deng Dau Deng, wanda shugaba Kiir ya sallama, bayan ya rike ma’aikatar tun daga watan Maris din farkon shekarar nan.  (Saminu Alhassan)