logo

HAUSA

AU ta dakatar da Gabon daga shiga ayyukan kungiyar

2023-09-02 16:20:22 CMG Hausa

Sakamakon juyin mulkin soji a kasar Gabon, hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka ta AU, ta sanar da dakatar da Gabon din daga shiga ayyukan kungiyar, har sai an dawo da aiki da kundin tsarin mulkin kasar.

Kaza lika, hukumar zartaswar kungiyar ta AU, ta yi kira da a gaggauta saki, tare da kare hakkokin shugaban kasar da aka hambarar. A kuma martaba kimar sa, da kare lafiyar sa, da ta iyalan sa, da ma sauran mambobin hambararriyar gwamnatin ta shugaba Ali Bongo.

Bugu da kari, hukumar ta AU, ta yi Allah wadai da kame jami’an tsohuwar gwamnatin bisa dalilai na siyasa, tana mai jaddada muhimmancin tabbatar da gabatar da fursunonin siyasar kasar gaban kotu, idan har akwai wani zargi a kan su, kamar dai yadda dokokin kasar suka tanada. (Saminu Alhassan)