logo

HAUSA

Za a fara amfani da motocin bus masu amfani da makamashin CNG a jihar Adamawa

2023-09-01 10:15:47 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya ta sayo motocin bus guda 10 masu amfani da makamashin CNG domin saukakawa al’ummar jihar wahalhalun sufuri.

Motocin kirar kamfanin gida na INNOSON ta sayo su kan tsabar kudi sama da Naira biliyan 1, tuni kuma motocin suka iso birnin Yola, fadar gwamnatin jihar inda ake jiran lokacin kaddamar da fara amfani da su.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

A lokacin da take karbar motocin a madadin gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, mataimakiyar gwamnan jihar Farfessa Kale-tapwa George Farauta ta ce, sayo motocin yana daya daga cikin alkawuran da gwamnan jihar ya dauka ne a jawabinsa na farko bayan rantsuwa.

“A madadin gwamnan ina tabbatar da cewa, za a yi amfani da wadannan motoci ta hanyar da ya kamata, kuma ’yan Adamawa ne za su ci gajiyarsu. Mun zo ne domin mu hidimta musu. Fatanmu a nan shi ne muna son kowane dan Adamawa ya dauka wannan gwamnati tasa ce. Akwai bukatar a hada hannu wuri guda domin marawa duk wasu manufofi da gwamnati ta bullo da su, don ta haka ne jihar za ta rinka samun ci gaba a kai a kai.”

Da yake nasa jawabi, shugaban kamfanin kira motoci na INNOSON Dr. Innocent Chukwuma, wanda ya samu wakilcin manajan kasuwanci na kamfanin Mr Obun Osigwe ya ce, “A madadin wannan kamfani, muna mika godiyarmu ga al’ummar jihar Adamawa bisa amincewa da amfani da motocinmu, wannan abun burgewa ne mutuka.” 

Dukkan motocin dai suna amfani ne da makamashin gas na CNG ko da yake har yanzu tasoshin samar da wannan makamashi ba su yawaita ba matuka a Najeriya. (Garba Abdullahi Bagwai)