logo

HAUSA

Za a rantsar da Brice Oligui Nguema a matsayin shugaban rikon kwarya na kasar Gabon

2023-09-01 15:34:50 CMG Hausa

Za a rantsar da Brice Oligui Nguema a matsayin shugaban rikon kwarya na kasar Gabon a ranar Litinin mai zuwa, a kotun kundin tsarin mulkin kasar dake fadar shugaban kasa.

Kakakin kwamitin gwamnatin riko da farfado da hukumomi na kasar (CTRI), Manfoumbi Manfoumbi ne ya sanar da haka a jiya Alhamis.

Brice Nguema wanda shi ne shugaban kwamitin CTRI, ya yanke shawarar farfado da kotun kundin tsarin mulki na wucin gadi da kuma kafa hukumomin rikon, tare da mayar da zirga-zirgar jiragen sama. Ya kuma bukaci ministocin gwamnati su tabbatar da komawa aiki nan take, tare da ci gaba da gudanar da ayyukan hidimtawa jama’a. (Fa’iza Mustapha)