logo

HAUSA

Sakatare janar na MDD ya yi gargadin juyin mulki a Afrika zai kara ta’azzara matsaloli

2023-09-01 10:06:08 CMG

Sakatare Janar na MDD Antonio Guteress, ya nanata muhimmancin tabbatar da shugabanci mai dorewa ta hanyar demokradiyya kuma bisa doron doka a kasashen nahiyar Afrika.

Antonio Guteress ya bayyana haka ne lokacin da yake tsokaci game da jerin juyin mulkin da aka yi a kasashen Afrika, yayin wata hira da manema labarai a hedkwatar MDD dake birnin New York.

Juyin mulkin da aka yi ranar Laraba a Gabon, ya zo ne bayan makamanciyarsa da aka yi cikin watan Yulin da ya gabata a Jamhuriyar Niger da kuma wanda aka yi a bara a Burkina Faso, sai na kasashen Chadi da Guinea da Sudan da Mali da aka yi a shekarun baya.

A cewar Antonio Guterres, kasashe da dama na fuskantar kalubalen shugabanci mai zurfi, amma kafa gwamnatin soji ba ita ce mafita ba. Yana mai cewa sojoji za su kara ta’azzara matsaloli, ba za su iya samar da mafita ba, sai kara tsananta yanayi.

Ya kuma yi kira ga kasashe da su dauki matakan da suka dace na kafa tsare-tsaren demokradiyya masu aminci, tare da tabbatar da dokoki.

Har ila yau, ya bayyana bukatar da ke akwai ta karfafa hukumomin kasa da kasa irinsu Tarayyar Afrika, wajen taka muhimmiyar rawa ta fuskar inganta zaman lafiya da tsayayyar demokuradiyya da ma shugabanci a Afrika. (Fa’iza Mustapha)