logo

HAUSA

Afreximbank: Nahiyar Afrika na cin moriyar kudaden cikin gida wajen hada-hadar kasuwanci

2023-08-31 10:06:45 CMG Hausa

Bankin kula da harkokin shige da fice na Afrika wato Afreximbank, ya ce nahiyar na cin moriyar amfani da takardun kudade na cikin gida wajen hada-hadar kasuwanci a tsakanin kasashenta.

Mataimakin shugaban sashen kula da harkokin kudi da tafiyar da mulki da samar da hidimomi na bankin, Denys Denya ne ya shaida hakan yayin wani shirin wayar da kai a Nairobin Kenya, inda ya ce yanzu haka ana fuskantar karancin kudaden ketare kamar dala, wadda aka saba amfani da ita a harkokin cinikayya tsakanin kasa da kasa.

Ya kara da cewa, amfani da kudaden cikin gida na da dimbin alfanu saboda yana rage yiwuwar fuskantar takunkumai daga kasashen da suka mallaki kudaden.

Har ila yau, ya ce kudaden cikin gida na bunkasa cinikayya tsakanin kasashen Afrika saboda ana bukatar dala ne kadai wajen biyan kudin sauyin da za a samu a lokacin cinikayya.

A cewarsa, tsarin biyan kudi na nahiyar Afrika da bankin Afrexim ya samar kuma manyan bankunan kasashen nahiyar ke amfani da shi, ya saukaka cinikayya tsakanin kasashen. (Fa’iza Mustapha)