logo

HAUSA

Majalissar dokokin Najeriya ta fara bin diddigin yadda manyan makarantun kasar suka sarrafa sama da naira Triliyan biyu

2023-08-31 14:04:51 CMG Hausa

Kwamitin majalissar wakilan Najeriya mai bibbiyar yadda asusun bunkasa ilimi a manyan makarantun kasar TETFUND ya sarrafa tsabar kudi naira triliyan 2 da miliyan 300 da gwamnati ta samar masa ya ziyarci jihar Sokoto domin binciken yadda aka kashe naira biliyan 40 da asusun ya turawa jihar.

Ziyarar da ta biyo bayan yawan zargin almundahna da ake yi wajen ayyukan da aka tsara yi da kudaden a wasu makarantun kasar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Majalissar wakilan dai ta kafa kwamitin ne tare da bashi damar zagaya dukkan manyan makarantun dake tarayyar Najeriya bisa shakkun da take da shi na amfani da kudaden ta hanyar da suka dace.

Hon Zakariya Dauda Yanfa shine jagoran kwamitin duba makarantun dake arewa maso yammacin kasar.

“wannan dalilin zuwan mu akwai kudi da ake ce masa TETFUND wato kudade na musamman da ake tarawa daga harajin `yan Najeriya wanda wannan kudin ya kai tiriliyan biyu da miliyan 300 kuma an baiwa makarantu da yawa ne a Najeriya kowacce jiha akwai tallafin kudi domin gine gine, mu kuma a majalissar an ce wannan kudin da ake turawa ana aiki da su kamar yadda ya kamata ko kuma a’a, shi yasa aka ce mana mu zo mu duba an yi ayyukan, in an yi to suna da inganci ko babu, sannan kuma mu duba mu ga cewa shin wannan tallafin a cigaba da shi ne ko kuma akai matsala”

‘Yan kwamitin dai sun ziyarci gwamnan jihar Sokoto Alhaji Ahmed Aliyu Sokoto, inda ya yabawa majalissar dokokin ta kasa saboda wannan yunkuri da ta yi na tabbatar da ganin ana gwada adalci da gaskiya wajen tafiyar da dukiyar al`umma.

“Wannan kwamitin ya zo daidai wurin da gwamnatin jihar take bukatar shigowa a tabbatar da cewa an yi al`ummar ta  adalci game da tallafin kudin da aka amsa na kusan kudin biliyan 40 daga wannan hukumar mai kula da manyan makarantun ilimi, babu shakka na gaya kwamiti duk wani hadin kai da ya kamata gwamnatin sa ta basu da kuma jami’an dake aiki karkashin ma’aikatar zasu bashi dari bisa dari, amma dai abun da ya shafi cin hanci ko daukar kudin jama` a ba bisa ka`ida ba ba tare da an yi masu aiki abu ne da wanda gwamantin da ke ci yanzu ba zata ta lamunce da shi ba”

‘Yan kwamatin dai zasu shafe sama da mako guda suna gewaya wa manyan makarantun daban daban dake jihar Sokoto.(Garba Abdullahi Bagwai)