logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sha alwashin kammala katafaren aikin titin Abuja zuwa Kaduna cikin shekarar badi

2023-08-30 09:10:38 CMG Hausa

Ministan ayyukan tarayyar Najeriya Sanata David Umahi ya tabbatarwa ’yan Najeriya cewa zuwa karshen shekara ta 2024 za a kammala aikin hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Ministan ya tabbatar da hakan ne a Kaduna a ci gaba da rangadin da yake yi zuwa duba mizanin ci gaban da aka samu a aikin manyan tituna da gwamnatin tarayyar ke gudanarwa a shiyoyi 6 na kasar, inda yace aikin daya taso daga Abuja zuwa Kano, amma Abuja zuwa Kaduna ne kawai ba a cimma komai ba. 

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

A lokacin da ya ziyarci mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna Dr Hadiza Sabuwa Balarabe, ministan ya ce, aikin da aka bayar da kwangilar tun a shekara ta 2017 amma kuma abun takaici akwai bangarorin da har yanzu ba a kai ga cimma kaso 20 na aikin ba.

“Baya ga wannan rangadi da na kawo yau zan sake dawowa domin duba wasu ayyukan da ake gudanarwa karkashin kulawar ma’aikata ta a wannan jiha, kuma  duka wannan rangadi ina yinsa ne bisa umarnin shugaban kasa, hakan ya nuna irin muhimmancin da wannan shiyya ke da shi a wajensa.” 

A lokacin da take jawabi, mataimakiyar gwmanan jihar Kaduna Dr Hadiza Balarabe ta yaba matuka bisa kudirin gwamnatin tarayyar na ganin cewa an dawo da aikin Abuja zuwa Kaduna gadan-gadan. Ta ce, babu shakka kuma aikin idan har an kammala shi zai kawo sauki ga masu ababen hawa sannan kuma zai yi maganin ayyukan ’yan ta’adda.

“Gwamnatin da al’ummar jihar Kaduna suna kira gare ka cewa ziyarar aiki na biyu da za ka sake kawowa a duba yiwuwar karasa mana aikin babban titin da ya yiwa garin Kaduna kawanya wanda aka bada aikinsa tun a shekara ta 2002, sannann kuma aka sake sabunta kwangilar aikin a shekara ta 2017 da zummar cewa za a kammala shi a shekara ta 2021.” (Garba Abdullahi Bagwai)