logo

HAUSA

Tinubu: Ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen tsige duk ministan da ya gaza taka rawar gani

2023-08-29 09:49:13 CMG Hausa


Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce, bukaci sabbin ministocinsa da su zage damtse wajen sauke nauyin kasa da aka rataya masu, ta hanyar yiwa al’ummar hidima tare da samar da kyakkywar makoma ga kasa.

Ya bukaci hakan ne jiya Litinin 28  ga wata yayin taron majalissar zartaswa na farko da ya jagoranta a fadarsa dake birnin Abuja, ya ce, mizanin ci gaba da kasancewar kowanne minista kan mukaminsa shi ne aiki tukuru ba tare da nuna kasala ko son azurta kai ba.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shaidawa ministocin cewa yanzu ragamar samar da makoma ta-gari ga kasa ya dogara ne a wuyansu, a don haka wajibi ne su baiwa mara da kunya ta hanyar nuna kwazo da kuma sanin makamar aiki.

Ya ci gaba da cewa, ko kadan ’yan Najeriya ba za su taba yi musu afuwa ba muddin dai aka samu nakasu ta wajen gaza tabbatar da kyakkyawan zaton da ake yiwa sabuwar gwamnatin.

Shugaba Tinubu ya bayyanawa ministocin nasa cewa, “Dukkannin mu nan muna da basira, muna da kwarewa da sanin yadda za mu bunkasa kasarmu, kuma ku sa ni fa burin ’yan kasa a kan wannan gwamnati yana da yawa matuka, a don haka sai mun dage sosai mun yi aiki tukuru wajen kirkiro sabbin matakan tattalin arziki masu fa’ida da za su amfani kowanne dan Najeriya.”

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kara da cewa wajibi ne mu san yadda za mu alkinta albarkatun da suke jibge a sassa daban daban na Najeriya ta yadda rayuwar al’umma za ta kara ingantuwa.

“Dole mu fara samar da abubuwa da kanmu, sannan kuma mu mayar da hankali ga harkar ilimi, kiwon lafiya, zuba jari a kan harkokin kyautata rayuwa da zamantakewa wadanda suna da muhimmanci ga ci gaba mutanenmu.”

Shugaban ya kara da bayanin cewa, a shirye yake ya karbi gyara idan ya yi kuskure domin Allah ne kadai baya kuskure, amma kuma ya ja hankalin ministocin cewa, kada su nuna fargaba a duk lokacin da za su zartar da wata manufa ta gwamnati, domin dai haka shugabanci ya gada. (Garba Abdullahi Bagwai)