logo

HAUSA

Tattaunawar bangarori uku kan takaddamar madatsar ruwan Nilu ta kawo karshe ba tare da cimma wani sakamako mai ma'ana ba

2023-08-29 09:52:26 CMG Hausa

Ma'aikatar albarkatun ruwa da ban ruwa ta Masar ta bayyana cewa, an kammala shawarwarin karshe kan takaddamar babbar madatsar ruwan kasar Habasha (GERD) a birnin Alkahira, ba tare da cimma wani sakamako na hakika ba.

A ranar Lahadin da ta gabata ce, dai aka dawo da yin tattaunawar da ta cije a tsakanin kasashen uku wato Masar, da Habasha, da Sudan a birnin Alkahira na kasar Masar, kan takaddamar da aka dade ana tafkawa dangane da babbar madatsar ruwan ta GERD.

Sanarwar bayan taron ta kara da cewa, kamata ya yi dukkan bangarorin da ke tattaunawa, su yi amfani da hangen nesa da za ta kai su ga yin tunani mai kyau, kan zagayen tattaunawar da za a yi. (Ibrahim)