logo

HAUSA

Hukumar NDLEA a jihar Katsina ta kara tsananta binciken miyagun kwayoyi a ababen hawa

2023-08-28 09:50:41 CMG Hausa

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a jihar Katsina ta kara matsa kaimi wajen binciken motocin fasinja da na dakon kaya da suke shigowa jihar domin rage yaduwar miyagun kwayoyi a jihar.

Mataimakin kwamandan hukumar a jihar mai kula da rage ta’ammali da miyagun kwayoyi da safararsu malam Mustafa Maikudi ya shaidawa taron manema labarai a karshen makon jiya a birnin Katsina cewa, hukumar ta lura yanzu dillalan miyagun kwayoyi sun fi amfani da motocin fasinja wajen shigo da kwaya cikin birnin Katsina da sauran manyan garuruwan dake jihar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Malam Mustafa Maikudi ya ce, baya ga binciken ababen hawa, jami’in hukumar kuma suna shiga garuruwa daban daban dake jihar ta Katsina, inda suke wayar da kan jama’a game da illar dake tattare da ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma bayar da kariya ga dillalan kwayoyin.

Mataimakin kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar ta Katsina ya ci gaba da cewa,“Wanda idan da muna da isassun kayan aiki da kuma motoci, to za mu iya kara wasu ofisoshi a cikin jihar Katsina. Yanzu  duk kananan hukumomi 6 muna da ofishin shiyya guda 1 ne kawai, ka ga aikin ya yi musu yawa, kuma ba za a je inda ya kamata a je ba. To amma da a ce muna da wadatattun ma’aikata da kuma kayan aiki ya kamata a ce, ko da ba mu yi irin yadda ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro suke yi ba inda suke da ofisoshi a kowacce karamar hukumar, to mu ya zama duk kananan hukumomi 2 ya zama muna da ofis guda to za ka ga cewa aikin zai kai har inda ba ya kaiwa da, amma yanzu a ce kananan hukumomin Mani, Mashi, Baure, Zangon Mai Aduwa, Sandamu da Bindawa, duk suna karkashin Daura to ka ga aikin ya yi musu yawa, amma idan aka ce an samu an rarraba to ka ga aikin zai iya kaiwa wuraren.”

To sai dai malam Mustafa Maikudi ya bayyana damuwar cewa wasu al’ummomi a jihar ba sa baiwa jami’an hukumar hadin kai wajen tona asirin mabuyar dillalan miyagun kwayoyin. Lamarin da yake kawo cikas sosai ga gudanarwar aikin jami’an hukumar cikin sauki. (Garba Abdullahi Bagwai)