logo

HAUSA

Bankin samar da ci gaba na Sin da bankin shige da fice na Afirka sun sanya hannu kan yarjejeniyar rancen kudi

2023-08-28 21:04:02 CMG Hausa

A yau Litinin ne bankin samar da ci gaba na Sin, da bankin shige da fice na Afirka, suka sanya hannu kan yarjejeniyar samar da rancen kudi na musamman har dalar Amurka miliyan 400, domin tallafawa wajen bunkasa kanana da matsakaitan kamfanoni dake nahiyar Afirka.

An dai sanya hannu kan yarjejeniyar samar da kudaden rancen ne a birnin Alkahirar kasar Masar. Ana kuma sa ran yin amfani da kudaden lamunin wajen inganta yanayin samar da kudade ga kanana da matsakaitan kamfanonin dake Afirka, ta yadda za su samu zarafin cin gajiyar hidimomin kudi masu yalwa, cikin sauki da kyawawan ka’idoji. Kaza lika matakin zai ingiza bunkasar tattalin arziki, da cinikayya, da hadin gwiwar hada hadar kudade tsakanin Sin da kasashen Afirka. (Saminu Alhassan)