logo

HAUSA

Majalisar dokokin Afrika ta kudu ta jinjinawa ci gaban da aka samu yayin taron kolin BRICS

2023-08-27 16:02:15 CMG HAUSA

 

Majalisar dokokin kasar Afrika ta kudu, ta fitar da wata sanarwa a jiya Asabar, wadda ke jinjinawa ci gaban da aka samu, yayin taron kolin shugabannin BRICS karo na 15.

Sanarwar ta ce, ganawar da aka yi a wannan karo na da muhimmanci matuka, kuma ci gaban da aka samu na shaida karfin jagoranci mai cike da hangen nesa, da alkawarin da shugabannin BRICS suka yi, kuma hakan ya bayyana ruhin hadin gwiwar kasa da kasa mai karfi, da nanata manufar gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban, da warware matsaloli cikin lumana, da ma samun ci gaba mai dorewa.

Ganawar ta mayar da hankali ga magance matsalar rashin daidaito a fannin tattalin arziki, da ingiza bunkasuwa, da bullo da manufofin hada-hadar kudi mai kunshe da kirkire-kirkire, matakin ba ma kawai zai inganta karfin mambobin BRICS ba ne, har ma zai aza ingantaccen tubulin ci gaba da dorewa ga nahiyar Afrika, har ma da dukkanin fadin duniya baki daya.

Ban da wannan kuma, sanarwa ta ce, ana ba da misali ta fuskar samun bunkasuwa cikin daidaito, da fahimtar al’adu, da yin hakuri da juna ta fuskar hadin kai da sauransu, ta hanyar karfafa gwiwar mu’ammalar al’adu, da bukatun kasashe maso tasowa, da yiwa tsarin hada-hadar kudin duniya kwaskwarima, ta yadda za a karfafa bunkasuwar tattalin arziki, da huldar abokantaka, tare kuma da shimfida yanayin duniya mai jituwa.

Kaza lika, sanarwar ta yaba shawarar da BRICS ta gabatar, ta habaka yawan mambobinta. Sanarwar ta ce, kara shigo da mambobi ya shaida cewa, kasashen BRICS na dukufa kan hakuri da juna, da gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban, da samun bunkasuwa tare. (Amina Xu)