logo

HAUSA

Hare-haren ’yan bindiga ya janyo shafe watanni 7 ana rufe makarantu a karamar hukumar Rijau ta jihar Neja

2023-08-27 15:55:34 CMG HAUSA

 

Iyayen yara a yankin karamar hukumar Rijau ta jihar Neja sun koka kan yadda rufe makarantun sakandire da aka yi na tsawon watanni 7 a yankin ke haifar da koma baya a fannin karatun ’ya’yansu.

Sama dai da makarantu 20 ne gwamnati ta bayar da umarnin rufewa tun farkon wannan shekara bayan da ayyukan ’yan ta’adda ke kara ta azzara a yankin.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.