logo

HAUSA

Shugaba Mnangagwa ya lashe zaben da aka kada a makon jiya

2023-08-27 15:41:01 CMG Hausa

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya lashe babban zaben kasar sa da aka kada a ranaikun 23 zuwa 24 ga watan nan, da kaso 52.6 bisa dari na jimillar kuri'un zaben, kuma da wannan nasara zai zarce kan karagar mulkin kasar a karo na biyu, inda zai shafe karin shekaru 5.

A cewar hukumar zaben kasar ZEC, shugaba Mnangagwa ya doke sauran 'yan takara 10 da suka shiga zaben na shugabancin kasa, inda ya samu yawan kuri'u da suka kai 2,350,711.

Shugabar hukumar ta ZEC Priscilla Chigumba, ta ayyana shugaba Mnangagwa Emmerson Dambudzo, na jam'iyyar ZANU-PF a matsayin wanda ya lashe zaben kasar, tun daga jiya Asabar 26 ga watan nan. Baya ga kujerar shugaban kasar, jam’iyyar sa ta ZANU-PF ta kuma samu rinjayen lashe kujerun majalissar dokokin kasar 210.

Rahotanni sun ce yayin zaben na ranaikun Laraba da Alhamis din makon jiya, al'ummar Zimbabwe da suka cancanci kada kuri'u kaso 68.9 bisa dari ne suka fita rumfunan zabe, inda suka kada kuri'un zaben shugaban kasa, da 'yan majalissun dokoki, da kuma wakilan kananan hukumomi.  (Saminu Alhassan)