logo

HAUSA

Gwamnatin sojin Nijar ta umarci jakadan Faransa da ya fice daga kasar cikin sa'o'i 48

2023-08-26 15:57:23 CMG Hausa

 

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Nijar ta fitar jiya Jumma’a, gwamnatin mulkin sojan kasar ta umarci jakadan kasar Faransa dake Nijar, da ya fice daga kasar cikin sa'o'i 48.

Amma kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito cewa, ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta bayyana a daren jiya cewa, ba za ta amince da bukatar gwamnatin mulkin sojan Nijar din ba, tana mai cewa, gwamnatin sojan kasar ba ta da hurumin umurtar Faransa da ta janye jakadanta daga kasar.

Wata sabuwa kuma, kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka wato ECOWAS ta bayyana a jiyan cewa, tana kokarin ganin an samar da mafita cikin ruwan sanyi domin dawo da kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar.

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar ECOWAS, Omar Alieu Touray ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai a birnin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, yana mai cewa, burin al'ummar Nijar zai iya samuwa ne kawai ta hanyar dimokuradiyya da kuma gudanar da harkokin mulki cikin hadin gwiwa.

Har ila yau a cewar Florencia Soto Nino, mai magana da yawun babban sakataren MDC Antonio Guterres, halin da ake ciki a jamhuriyar Nijar ya sanya janyewar dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD (MINUSMA) daga makwabciyarta Mali ta kara dagulewa.

Ta bayyana cewa, har yanzu dai abubuwa suna tafiya yadda ya kamata. Don haka kungiyar ta duniya tana duba dukkan damar da ake da ita a yankin ya zuwa yanzu. (Ibrahim)