logo

HAUSA

Ci gaban dangantakar Sin da Afirka ya kama hanyar bunkasa cikin sauri

2023-08-24 20:59:42 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a yayin taron manema labaru na yau da kullum Alhamis din nan cewa, tun lokacin da shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar samar da sahihan manufofin, abokantaka, da sahihanci ga nahiyar Afirka, da ma'anar adalci da moriya a shekarar 2013, bunkasuwar dangantakar Sin da Afirka ta kama hanyar bunkasa cikin sauri.

Rahotanni na cewa, yawan darajar da ba ta shafi cinikayya ba a watanni 7 na farkon bana, ya kai RMB tiriliyan 1.14, adadin da ya karu da kashi 7.4 bisa 100 kan na shekarar bara, wanda ke nuna kyakkyawan ci gaban hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. Kamar yadda Wang Wenbin ya bayyana a yayin da yake amsa tambayoyin kan wannan batu.

Wang ya ce, yayin taron shugabannin kasashen BRICS, shugaba Xi Jinping da takwaransa na Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, za su jagoranci taron shugabannin kasashen Sin da Afirka. Ya yi imanin cewa, a karkashin jagoranci da karfafa gwiwar shugabannin diplomasiyya, gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka a sabon zamani, ba shakka, za ta cimma sabbin nasarori masu dimbin tarihi, don ba da babbar gudummawa wajen inganta zamanantar da dan Adam, da bunkasuwa, da samar da wadata, da ci gaba. (Ibrahim Yaya)