logo

HAUSA

Xi:Sin tana goyon bayan Malawi wajen lalubo hanyoyin samun ci gaba da ya dace da yanayin kasarta

2023-08-24 21:00:31 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi ya bayyana a yau Alhamis cewa, kasar Sin tana goyon bayan kasar Malawi wajen nazarin hanyar samun bunkasuwa da ta dace da yanayin kasarta, kuma a shirye take ta ci gaba da baiwa Malawi duk wani taimako da za ta iya yi, a fannin raya zamantakewar al'umma da tattalin arziki.

Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da takwaransa na kasar Malawi, Lazarus Chakwera, a gefen taron kasashen BRICS karo na 15. (Ibrahim Yaya)