logo

HAUSA

CMG da kamfanin watsa labaran Afirka ta kudu za su yi hadin gwiwar shirya shirin talabijin na “documentary”

2023-08-24 10:53:28 CMG Hausa

Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG da hadin gwiwar kamfanin watsa labarai na kasar Afirka ta kudu, sun sanar da aniyar su ta shirya wani shirin talabijin mai kunshe da al’amaru na gaske, ko “Documentary”, wanda aka yiwa lakabi da “Shekaru 25 na kawance da hadin gwiwar Sin da Afirka ta kudu”.

A jiya Laraba ne dai aka bayyana hakan a hukumance, kuma shirin zai yi bitar yadda Sin da Afirka ta kudu ke kokari tare, wajen gina babbar al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama.

Mataimakin ministan ma’aikatar yada manufofi ta kwamitin kolin JKS, kuma shugaban CMG Shen Haixiong, da wakiliyar babbar jami’ar kamfanin watsa labarai ta kasar Afirka ta kudu uwar gida Nada Wotshela, kuma babbar jami’ar harkokin kudin kamfanin Yolandi van Biljon, su ne suka jagoranci kaddamar da aikin, tare da ganewa idanun su musayar takardun kulla yarjejeniyar sa. (Saminu Alhassan)