logo

HAUSA

Masana: Najeriya za ta fi kowacce kasa a Afrika cin moriya ta fuskar diplomasiyya idan ta samu shiga kungiyar BRICS

2023-08-24 14:47:12 CMG Hausa

A daidai lokacin da ake daf da karkare taron koli na kungiyar kasashen BRICS, masu sharhi kan harkokin diplomasiyya a Najeriya sun hango cewa, Najeriya a matsayinta na mafi karfin tattalin arziki a Afrika, za ta samu moriya mai yawan gaske fiye da irin wanda take samu ta mu’amullarta da kasashen yammacin Turai.

A ci gaba da jin ra’ayoyin ’yan Najeriya da wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ke yi game da tasirin shigar Najeriya cikin kungiyar ta BRICS, a yau ya ji ra’ayi daya daga cikin fitattun masu fashin baki kan harkokin diplomasiyyar kasa da kasa Malam Bash M. Bash, inda ya ce, alakar Najeriya da kasashen BRICS za ta yi tasiri sosai ta fuskar cin moriyar  ba tare da kwarar juna ba.

Ga dai Malam Bash M. Bash da sauran kalamansa a firarsa da wakilinmu dake Najeriya Garba Abdullahi Bagwai.

“To idan muka samu fahimtar juna da kuma tabbatar da duk wata alaka da za ta amfani juna a kan matsayin raba daidai, kai ka amfana ni na amfana, na tabbata idan BRICS  ta karfafa, aka kulla alaka ta diplomasiyya da kasashen da suke son zama membobinta, Najeriya a matsayin wadda take da karfin tattalin arzikin kasa a Afrika, to tana da rawar da za ta taka, su kuma wadannan manyan kasashen da suke cikin BRICS, ai su kan hararo da idon kallo, cewa wadannan kasashe wadanda suke da karfin tattalin arzikin kasa a nahiyar Afrika da sauran nahiyoyi na duniya, to za su iya zama abokan tafiya wajen ganin an hada karfi da karfe wajen cimma bukatu da moriyar juna ta fuskar diplomasiyya, kamar yadda na fahimci yanayin tsarin kasar CHINA.

Idan ka duba siyasar tattalin arzikin kasar China, in ka yi alaka da shi da yadda ya shafi duniya, Najeriya za ta amfana kwarai da gaske.