logo

HAUSA

Wakilin ECOWAS ya bayyana kyakkyawar ra’ayi game da warware rikicin Nijar ta hanyar diflomasiyya

2023-08-23 11:00:18 CMG Hausa

Manzon musamman na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, Abdulsalam Abubakar, ya sanar a jiya Talata cewa, an kusa cimma matsaya ta hanyar diflomasiyya don warware rikicin da ta dabaibaye kasar Nijar.

Abubakar, wanda ya gana da shugaban Najeriya Bola Tinubu kuma shugaban kungiyar ECOWAS na yanzu a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, domin gabatar da rahoton ziyarar da ya kai Nijar a kwanakin baya, ya shaidawa manema labarai cewa an samu ci gaba a tattaunawar da aka yi da gwamnatin mulkin soja na kasar Nijar.

Abdulsalam Abubakar ya ce, ziyarar da suka kai Nijar ta yi matukar amfani kuma ta bude hanyar fara magana, kuma da fatan za a samu maslaha.

A wani taron da aka gudanar a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar a ranar Asabar din da ta gabata, Abubakar wanda ya jagoranci wata tawaga ta musamman ta kungiyar ECOWAS a yunkurinta na magance matsalar zamantakewa da siyasa, ya yi tattaunawa mai zurfi da gwamnatin mulkin soja dake rike da madafun iko a halin yanzu. (Mahammed Baba Yahaya)