logo

HAUSA

Guguwar iska mai karfi ta lalata wani gidan gona tare da hallaka kaji kusan dubu 12 a Najeriya

2023-08-22 09:32:45 CMG Hausa

Iska da ruwan sama mai karfin gaske sun yi sanadin lalacewar wani gidan gonar kiwon kaji dake Rapomol a yankin karamar hukumar Barikin Ladi dake jihar Filato a arewa ta tsakiyar Najeriya, inda a kalla kusa kaji dubu 12 suka mutu.

Lamarin ya faru ne a daren Lahadi 21 ga wata, manyan dakuna 6 na  kiwon kaji ne suka lalace, da kejin kiwo na zamani mai amfani da wutar lantarki da kuma turakun wutan lantarki da suka kareraye inda aka kiyasta asarar sama da Naira miliyan 250.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

A lokacin da yake zagayawa da manema labaru bangarori daban daban da ruwan ya lalata, manajan darkatan gidan gonar Mr. Keneth Mafala ya ce, an fara amfani da gidan gonar ne tun a 1976 wanda kuma yana daya daga cikin fitattun gidajen gona dake jihar ta Filato.

Ya ce, adadin kaji dubu 60 ake kiwatawa a gidan gonar, kuma kaji masu kwai 10,800 ne suka mutu baya ga sauran kajin nama da kuma wadanda aka kyan-kyeshe.

“Fadin gidan gonar ya kai hekta 4.5 kuma akwai ma’aikata da ake biya albashi kusan 60, har ya zuwa yammacin jiya Litinin dai babu wani abu da gwamnati ta yi a kai, amma dai shugabancin kungiyar masu kiwon kaji ta kasa sun zo tare da ’yan jaridu domin duba asarar da aka yi a jiya Lahadi.”

A cikin wata sanarwar da suka fitar, kungiyar masu kiwon kaji ta tarayyar Najeriya reshen jihar Filato ta hannun shugabanta Madam Nanji Gambo ta bayyana alhininta kan abun da ya faru. (Garba Abdullahi Bagwai)