Shugaban Najeriya ya halarci bikin rantsar da sabbin ministocin gwamnatinsa
2023-08-22 10:26:22 CMG Hausa
A jiya Litinin ne shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya halarci bikin rantsar da sabbin ministocin gwamnatin sa, inda ya yi kira gare su, da su taka rawar gani wajen dawo da amincewar al’umma, da ingiza ci gaban kasa.
Cikin jawabin da ya gabatar yayin bikin rantsuwar wanda ya gudana a birnin Abuja, fadar mulkin kasar, Tinubu ya yi kira ga sabbin ministocin su 45, da su shigar da kwarewar da suke da ita a fannoni daban daban, cikin ayyukan ma’aikatun su, su kuma ba da karfi ga hadin gwiwa da sauran sassa masu ruwa da tsaki, wajen shawo kan manyan matsalolin dake addabar Najeriya.
Shugaba Tinubu, ya jaddada muhimmancin sauke nauyin dake wuyan su ta fuskar tsara manufofi, wadanda za su yi kyakkyawan tasiri ga rayukan miliyoyin al’ummar Najeriya.
Ya ce, “A wannan tafiya wadda nake jagoranta, tare da ‘yan Najeriya dake biye, ya zama wajibi ku mayar da moriyar daukacin al’ummar kasa gaban komai, kana ku sanya bukatun ‘yan kasa baki daya, sama da bukatun yanki ko wasu jihohi daidaiku. Dukkanin ‘yan kasa sun zura ido, yayin da ni da ku za mu sarrafa alakar wannan kasa”. (Saminu Alhassan)