logo

HAUSA

Ministan Zimbabwe: BRICS na samar da ci gaba ga abokan hulda

2023-08-21 14:18:01 CMG Hausa

Babban Jami’ar Zimbabwe ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya-baya nan cewa, BRICS ta zama abin sha'awa ga kasashe masu tasowa, kuma tana samar da ci gaba bisa adalci da gaskiya a harkokin cinikayyar duniya.

Kasashe masu tasowa na fuskantar kalubale iri-iri wadanda ke da alaka kai tsaye da rashin daidaiton hulda tsakanin kasashe da kungiyoyi yayin da wasu kasashe suka mamaye tsarin kasa da kasa a fannin kudi da soja don samun moriyarsu, in ji ministar yada labarai Monica Mutsvangwa.

Ta ce, Afirka na fama da katsalandan siyasa daga waje tsawon shekaru da dama, kamar yadda ake gani a halin yanzu a yankin yammacin Afirka, tare da munanan alamun tabarbarewar yankin.

Ta yi nuni da cewa, galibin kasashen dake kudu da hamadar Sahara sun san illar da shirye-shiryen masu ba da lamuni na duniya karkashin jagorancin kasashen yammacin duniya ke yi, kuma ba za su iya samun lamuni daga wadannan cibiyoyi na kasa da kasa ba, ba tare da an sanya mana tsauraran sharudda ba, in ji Mutsvangwa.

Ta kara da cewa, kasashe masu tasowa sun riga sun fara ganin wata damar ci gaba da samar da kudaden raya ababen more rayuwa ba tare da tsauraran sharudda ba ta hanyar BRICS. (Yahaya Babs)