logo

HAUSA

An kaddamar da shirin bidiyon “Bayanan magabata dake jan hankalin Xi Jinping” kashi na biyu a Afirka

2023-08-21 10:12:05 CMG Hausa

An shirya bikin kaddamar da shirin bidiyo mai taken “Bayanan magabata dake jan hankalin Xi Jinping” kashi na biyu, da babban rukunin rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG a takaice ya samar cikin harsuna da dama wadanda suka hada da Turanci da Faransanci da Larabci da Hausa da Swahili a jiya ranar 20 ga wannan wata a birinin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu a gabannin ziyarar aikin da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai yi a kasar, inda kuma zai halarci ganawar shugabannin kasashen mambobin kungiyar BRICS karo na 15. An kuma fara watsa shirye-shiryen a manyan kafofin watsa labarai 62 a kasashen Afirka 38 tun daga jiya Lahadi.

An zabi kalaman magabata da shugaba Xi ya ambata a cikin muhimman jawabai da bayanai da tattaunawa na sa, kalaman da suka nuna ilmomin al’adu masu zurfi da soyayyarsa ga al’ummun Sinawa.

Mataimakin shugaban jam’iyyar ANC kuma mataimakin shugaban kasar Afirka ta Kudu Paul Mashatile shi ma ya gabatar da wani jawabi a rubuce, inda ya taya CMG murnar gabatar da shirin bidiyon mai ma’anar tarihi.

Kana mataimakin shugaban ma’aikatar yada manufofin JKS kuma shugaban CMG Shen Haixiong ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, shirin bidiyon da ake gabatarwa zai bude wata taga ga aminan kasashen Afirka yayin da suke kokarin kara fahimtar tunanin tafiyar da harkokin kasa na shugaba Xi Jinping, haka kuma zai taimake su domin su kara fahimtar al’adu da hikima da kuma ruhi na kasar Sin. (Jamila)