logo

HAUSA

UNFPA za ta taimakawa mata a jihar Zamfara a fannin kiwon lafiya da ilimi da kuma zamantakewa

2023-08-21 09:28:46 CMG Hausa

Asusun kula da yawan al’umma na Majalissar Dinkin Duniya ya sha alwashin bada himma wajen agazawa rayuwar iyaye mata da kuma yara mata da tashe-tashen hankula ya yi sanadin kauracewa muhallansu a jihar Zamfara ta arewacin Najeriya.

Babbar jami’ar asusun dake kula da shiyyar Kaduna Mrs Loide Am-kongo ce ta tabbatar da hakan a karshen mako yayin wani zagaye gangamin wayar da kai da aka shirya a garin Gusau domin sheda ranar aiyukan jin kai na duniya na 2023.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Gangamin wayar da kai an shirya shi ne bisa hadin gwiwa da hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Zamfara, kuma an yi masa take da cewr “kowanne abu a duniya yana da nasa kalubale”.

Babbar jami’ar asusun Madam Loide Am-kongo ta ci gaba da cewa a yanzu haka asusun ya samar da asibitin tafi da gidanka a jihar ta Zamfara hususan domin duba mata masu juna biyu ’yan gudun hijira tare da karbar haihuwa su a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

(muryar Madam Loide Am-kongo)

A lokacin da yake jawabi, daraktan tsare-tsare na ma’aikatar ayyukan jin kai da ba da agajin gaggawa ta jihar Zamfara Alhaji Isa Shu’aibu ya yaba matuka bisa irin gudummawar da Asusun na UNFPA da sauran kungiyoyin agaji na kasa da kasa suke baiwa ’yan gudun hijirar jihar wadanda suke tsugune yanzu haka a wasu sansanoni.

A kan dalilan da suka sanya hankali ya fi karkata ga mata kuwa wajen bayar da agajin, Alhaji Isah Shu`aibu ya ce, 

“Mun lura da cewa mata su suka fi shiga yanayi, idan aka yi rikici aka kashe namiji, mace ake bari da dawainiyar ’ya’ya, yanzu haka ma akwai shirin bayar da tallafin kayan sana’o’in dogaro da kai wanda ma’aikatar jin kai ke shiryawa.”

Daga tarayyar Najeriyam Garba Abdullahi Bagwai, CRI Hausa. (Garba Abdullahi Bagwai)