logo

HAUSA

Dandalin Kafofin Watsa Labarai Na BRICS Karo Na 6 Ya Yi Kira Da A Karfafa Muryoyin Kasashe Masu Tasowa

2023-08-20 16:18:01 CMG Hausa

A jiya ne, aka bude taron dandalin tattaunawa na kafofin watsa labarai na kasashen BRICS karo na 6, a kasar Afirka ta Kudu, inda aka yi kira da a kara daga muryoyin kasashe masu tasowa.

Kimanin wakilai 200 daga kafafen watsa labarai kusan 100, da cibiyoyin bincike da kungiyoyin kasa da kasa daga kasashe kusan 30 ne suka tattauna a bisa taken "BRICS da Afirka: Karfafa Tattaunawar kafofin watsa labarai don samar da makomar bai daya ba tare da son zuciya ba."

A jawabinsa yayin bude taron, shugaban kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin, Fu Hua, ya bayyana cewa, kafofin watsa labarai na kasashen BRICS suna da babban nauyi a wannan zamani, kuma suna jin dadin yin hadin gwiwa matuka.

Fu Hua ya ba da shawarar inganta makomar bai daya ga daukacin bil-Adama, tare da inganta gina tsarin kasa da kasa mai cike da adalci da daidaito, da bayar da labarun BRICS masu kayatarwa a sabon zamani, da inganta mu'amalar al'adu da koyi da juna tsakanin al'ummomi.

A nasa bangaren kuwa, mamba a kwamitin zartarwa na majalisar wakilan jama'ar Afirka ta Kudu, Dakota Legoete, ya bayyana cewa, a yayin da wasu kasashe ke kokarin yin babakere a harkoki na kasa da kasa tare da amfani da kafafen watsa labarai wajen kai hari kan ‘yancin wasu kasashe masu cin gashin kai, kafofin watsa labaru na BRICS sun nuna cewa, kamata ya yi kafofin watsa labaru su himmatu wajen yayata ci gaban duniya, maimakon zama makami na haifar da yake-yake.(Ibrahim)