logo

HAUSA

Babban jami'in Afirka ta Kudu ya gana da shugaban CMG

2023-08-20 16:08:06 CMG Hausa

A jiya Asabar, mataimakin shugabar majalisar dokokin kasar Afirka ta Kudu, Solomon Lechesa Tsenoli, ya gana da shugaban babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin (CMG), mista Shen Haixiong, a Cape Town na kasar Afirka ta Kudu.

Yayin ganawarsu, mista Tsenoli ya taya CMG murnar kulla huldar hadin gwiwa tare da kamfanin MIH na kasar Afirka ta Kudu, kamfani mafi girma dake watsa shirye-shirye kai tsaye ta hanyar taurarin dan Adam a nahiyar Afirka. A cewar mista Tsenoli, al'ummun kasarsa na Allah-Allahr ganin ziyarar shugaba Xi Jinping na kasar Sin a kasar Afirka ta Kudu, kuma yana da imanin cewar, kasashen 2 za su iya cimma dimbin nasarori a hadin gwiwarsu, gami da taimakawa kokarin tabbatar da tsari mai adalci da kima a duniya.

A nashi bangare, mista Shen Haixiong ya ce, kamfanin CMG na son karfafa hadin kai tare da majalisar dokokin kasar Afirka ta Kudu, da zummar zurfafa abokantaka, da bayar da gudunmowa ga yunkurin gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya tsakanin kasashen 2.

Duk a wannan rana, kamfanin CMG na kasar Sin da kamfanin MIH na kasar Afirka ta Kudu, sun kulla yarjejeniyar hadin gwiwa a birnin Cape Town, inda CMG ya ba MIH izinin watsa shirye-shiryen tashoshinsa na CCTV-4, da CGTN-English, da CGTN-French, a kasashe fiye da 50 dake nahiyar Afirka. (Bello Wang)