logo

HAUSA

Gwamnatin kasar Qatar za ta gina gidaje har 500,000 ga marasa galihu a jihar Kaduna

2023-08-19 15:42:41 CMG Hausa

A jiya Juma’a 18 ga wata, gwamnatin jihar Kaduna tare da hadin gwiwa da kungiyar jin kai ta kasar Qatar, Qatar Charity Foundation suka kaddamar da aikin ginin gidaje 500,000 ga marasa galihu a jihar Kaduna.

A yayin bikin, gwamnan jihar kaduna Sanata Uba Sani ya yaba matuka ga ofishin jakadancin Qatar dake Najeriya saboda zabar Kaduna a matsayin daya daga cikin jihohin da za su ci gajiyar ayyukan jin kai da kasar ke gudanarwa a sassan duniya.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Gwamnan na jihar Kaduna ya ci gaba da cewa aikin ginin gidajen na daya daga cikin muhimman burikan gwamnatin jihar shekaru da dadewa karkashin shirinta na samarwa masu karamin karfin muhallin da ya kamace su.

“Za su tabbatar da ganin sun samu marayu sama da dubu daya sun ba su tallafi domin su yi karatu, haka kuma za su bayar da kayan sana’a ga mutane sama da dubu biyar.”

Da yake nasa jawabin, jakadan kasar Qatar a Najeriya Dr. Ali Bin Ghanem Al-Hajri ya ce, kasar ta Qatar za ta kashe miliyoyin daloli wajen gudanar da wannan aiki tare kuma da rarrabar kayayyakin sana’o’in hannu kamar injunan walda, da kekunan dinki, da kayan aski da na gyaran gashin mata, sanan kuma za a gina daruruwan rijiyoyin burtsatsai a kananan hukumomi 23 dake jihar ta Kaduna. (Garba Abdullahi Bagwai)