Shugabannin tsaro na ECOWAS sun gana domin tattauna shirin tura dakarun ko-ta-kwana zuwa Nijar
2023-08-18 09:34:09 CMG Hausa
A jiya ne, shugabannin tsaro na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka wato ECOWAS a takaice, suka hallara a birnin Accra na kasar Ghana, inda suka tattauna batun shirin tura dakarun ko-ta-kwana zuwa Jamhuriyar Nijar.
An dai bude zama na musamman na kwanaki biyu na kwamitin hafsan hafsoshin tsaron kungiyar ce, daga jiya Alhamis zuwa Juma'ar nan, biyo bayan umarnin da shugabannin kungiyar suka bayar, a taronsu na gaggawa na karshe da suka yi a Najeriya, domin tattauna halin da ake ciki a kasar ta Nijar.
Da yake bude taron, kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na kungiyar ECOWAS, Abdel-Fatau Musah, ya ce duk da shirye-shiryen da ake na tura rundunar ko-ta-kwana ta kungiyar, zabin soja zai kasance mataki na karshe, kuma duk wasu zabin da suka hada da kudurin diflomasiyya na nan a kan teburi.
Musah ya ce, a shirye rundunar ta ECOWAS take ta koma Jamhuriyar Nijar, domin maido da kundin tsarin mulkin kasar, idan har duk wani yunkuri na kawo karshen rikicin cikin lumana ya ci tura. (Ibrahim Yaya)