logo

HAUSA

Shugaban Uganda ya bayyana galibin tallafin kudade daga kasashen yamma a matsayin masu hana bunkasuwa

2023-08-18 11:25:48 CMG Hausa

Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya bayyana cewa, galibin lamuni da taimakon da ake samu daga kasashen yammacin duniya, ba su da wani amfani ga kasarsa ko ma suna hana ci gaba.

Shugaban ya bayyana cewa, galibin lamuni da tallafin ba su da wani amfani ga kasar ko kuma ma suna hana bunkasuwar kasar gaba daya, Museveni ya bayyana hakan ne, a wani martani na baya-bayan nan da ya mayar, game da matakin da bankin duniya ya dauka, na dakatar da samarwa kasar rancen kudi, bayan da ta aiwatar da dokar hana luwadi da madigo da ake cece-kuce a kasar dake gabashin Afirka.

Museveni ya bayyana a cikin wata sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar jiya Alhamis cewa, lamuni da tallafin da kasashen yammacin duniya suka bayar, sun kawo cikas matuka ga ci gaban Uganda da ma nahiyar Afirka baki daya.

A matsayin mafita, Museveni ya ce sojojin kasar, da ababen more rayuwa, da kamfanoni masu zaman kansu, da kuma babbar kasuwa a Afirka, da Sin, yankin gabas ta tsakiya da kuma Rasha, za su cike wannan gibi.

Shugaban ya kuma dora alhakin yanayi mai muni da tattalin arzikin Afirka ya shiga, a kan kasashen yammacin duniya, wadanda ke kallon Afirka kawai a matsayin masu samar da muhimman albarkatu. (Ibrahim Yaya)