logo

HAUSA

An kashe sojoji 36 a Nijeriya

2023-08-18 10:30:44 CMG Hausa

Jimilar sojoji 36 ne aka kashe yayin wata kwantar bauna da ‘yan ta’adda suka yi musu, haka kuma wani jirgin soji mai saukar ungulu ya fadi a jihar Niger dake yankin tsakiyar kasar.

Kakakin rundunar sojin Edwards Buba, ya shaidawa wani taron manema labarai jiya a Abuja babban birnin kasar cewa, wasu ‘yan ta’adda da ba a san su wanene ba, sun yi wa dakarun kwantar bauna a ranar Litinin, kusa da garin Zungeru na jihar, inda wasu sojoji suka mutu yayin da ake musayar wuta.

Haka kuma, wani jirgin soji mai saukar ungulu da aka yi amfani da shi wajen kwashe wadanda harin ya rutsa da su, ya fadi a kusa da inda aka yi wa sojojin kwantar bauna, lamarin da ya kai adadin sojojin da suka mutu a ranar Litinin, zuwa 36.

Ya kara da cewa, zuwa yanzu, ba a san musabbabin faduwar jirgin ba, amma ana ci gaba da gudanar da bincike. (Fa’iza Mustapha)