logo

HAUSA

A karon farko an kaddamar da aikin yiwa yara rijista ta amfani da na’ura mai kwakwalwa a jihar Sakkwato

2023-08-17 11:12:13 CMG Hausa

Hukumar kidayar jama’a ta tarayyar Najeriya tare da hadin gwiwa da hukumar wayar da kan jama’a ta kasa da kuma hukumar UNICEF sun kaddamar da shirin yiwa yara rijistar haihuwa ta amfani da na’urar kwamfuta a jihar Sakkwato.

Za a shafe tsawon makonni shida ana gudanar da aikin wanda yake da manufar tattara bayanan haihuwa da mutuwa a Najeriya kamar yadda yake kunshe a shirin muradun ci gaba na kasa da kasa.

Wakilinmu a tarayyar Najeriya Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

Kamar yadda aka tsara wadanda aikin zai shafa su ne jarirai da kuma yaran da shekarunsu bai wuce 17, inda za a shiga dukkan mazabu 277.

Kwamshinan tarayyar mai wakiltar Sakkwato a hukumar kidayar jama’a ta kasa reshen jihar, Alhaji Abdullahi Dattijo shi ne ya jogranci kaddamar da shirin a mazabar tudun wada dake jihar ta Sakkwato.

“Maimakon takarda da biro ko da fensir yanzu komai ana yinsa da na’urar telephone Android, ka ga abu ne na ci gaba kuma mu ba za mu yarda a bar mu a baya ba. Wannan abu da muka dauka za mu ci gaba da shi insha Allahu ba za mu kunyata Ssakkwato ba.”

Gwamnatoci dai na amfani da kididdigar jama’a wajen tsare-tsaren ayyukan ci gaba da suka kunshi kiwon lafiya.

Dr. Hadiza Yaro Bodinga ita ce babbar jami’a a hukumar kiwon lafiya matakin farko a jihar Sakkwato kuma tana daga cikin masu ruwa da tsaki wajen gudanar da aikin rijistar.

“Da wannan tsididdigar ita ce za a iya sanin asibiti nawa suke bukata, makarantu nawa suke bukata. Duk wani taimako da za a kawo a wannan wuri da irin wannan kiyasi ne za a yi amfani da shi a bayar da duk wata gudumawa da za a kawo ga wuri, domin idan babu wannan kiyasin, ta yaya za a san wane irin abu za a kawo a wurin.”

Kimanin yara sama da miliyan 12 ne da ake sa ran za a yi wa rijistar haihuwa a duk fadin tarayyar Najeriya, jihar Sakkwato kuma na daga cikin jerin jihohi 21 da aka fi baiwa fifiko a cikin shirin. (Garba Abdullahi Bagwai)