logo

HAUSA

Manyan hafsoshin tsaron ECOWAS za su gana kan batun tura dakaru Niger

2023-08-17 10:32:38 CMG Hausa

Manyan hafsoshin tsaron kungiyar ECOWAS mai raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, za su gana a birnin Accra na kasar Ghana, daga yau Alhamis zuwa gobe Juma’a, domin kammala shirin tura dakarun kungiyar zuwa jamhuriyar Niger.

Wata sanarwar da hukumar ECOWAS ta fitar, ta ruwaito cewa, taron na yini biyu na kwamitin manyan hafsoshin tsaron kasashen ECOWAS, ya biyo bayan umarnin da shugabannin kungiyar suka bayar yayin taron gaggawa da suka yi makon da ya gabata a birnin Abujan Nijeriya, kan yanayin siyasar Niger.

Yayin taron na makon da ya gabata, shugabannin kungiyar sun yanke shawarar dakarunsu za su kasance cikin shiri, domin martani ga juyin mulkin Nijer, yayin da suka kuma nanata ci gaba da kokarin mayar da kundin tsarin mulkin kasar bisa hanyoyi na lumana. (Fa’iza Mustapha)