logo

HAUSA

Har yanzu Amurka na mayar da hankali ga warware batun juyin mulkin Niger ta hanyar dilomasiyya

2023-08-16 10:07:03 CMG HAUSA

 

Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken, ya ce har yanzu Amurka na mayar da hankali kan matakan diflomasiyya a matsayin hanyar warware rikicin siyasa a Niger, sanadiyyar juyin mulki da sojoji suka yi.

Anthony Blinken ya bayyana haka ne a jiya Talata, inda ya ce Amurka na ganin ya zama wajibi shugabannin da suka yi juyin mulki su saki hambararren shugaban Mohamed Bazoum da iyalansa da suka tsare, haka kuma ya kamata a mayar da kundin tsarin mulkin kasar.

Ya ce a don haka, Amurka na bayar da goyon baya mai karfi ga abubuwan da kungiyar ECOWAS mai raya tattalin arzikin yammacin Afrika ke aiwatarwa.

Game da ko Amurka za ta goyi bayan amfani da karfin soji kamar yadda ECOWAS ta yi barazana, Blinken ya ce ba zai yi riga mallam masallaci ko misalta abun da zai faru a nan gaba ba. (Fa’iza Mustapha)