logo

HAUSA

Gwamnatin Kano ta kaddamar da dashen itatuwa har sama da miliyan daya

2023-08-16 09:56:18 CMG HAUSA

 

Gwamnatin jihar Kano dake arewacin Najeriya ta kaddamar da bikin dashen itatuwa na shekarar 2023 har sama da miliyan guda a wani mataki na aiwatar da yarjejeniyar Paris kan sauyin yanayi a duniya.

Da yake kaddamar da shirin, gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce, za a shafe makonni  biyu ana aikin dashen a sassan jihar, kuma itatuwan da za a dasa sun kunshi nau`ika daban daban.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.