logo

HAUSA

Masani na Kenya: Kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a kokarin ciyar da tsarin BRICS gaba

2023-08-16 11:02:14 CMG Hausa

Za a gudanar da taro karo na 15 na shugabannin kasashen tsarin hadin gwiwar BRICS, da ya kunshi kasashen Brazil, da Rasha, da India, da Sin, gami da Afirka ta Kudu, tsakanin ranar 22 da ta 24 ga wata, a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu. Dangane da taron, Stephen Ndegwa, darektan kungiyar musayar ra’ayi tsakanin kasashe masu tasowa ta kasar Kenya, ya ce, za a tattauna dimbin batutuwa masu muhimmanci a wajen taron, ta yadda za a taimakawa kasashe masu tasowa a kokarinsu na daidaita matsalolin da suke fuskanta.

Mista Ndegwa ya ce, daya daga cikin muhimman batutuwan da za a lura da su wajen taron dake tafe, shi ne yadda za a habaka tsarin BRICS, ganin yadda dimbin kasashe ke sha’awar shiga cikin tsarin. Ya ce hakan na nufin kasashe masu tasowa na kokarin koyon ingantattun fasahohi a fannin raya tattalin arziki. Haka zalika, za a iya tattauna batun kudi a wajen taron, ta yadda za a samu damar magance dogaro kan dalar Amurka.

Ban da haka, Stephen Ndegwa ya kara da cewa, kasar Sin kasa ce dake kan hanyar tasowa mafi girma a duniya, wadda ke taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da tsarin BRICS gaba. Ya ce yanzu haka, Sin tana kokarin taimakawa dimbin kasashe masu tasowa daidaita matsalolin da suke fuskanta, inda ta nuna musu cewa, za a iya daidaita wadannan matsalolin da aka dade ana fama da su, da kawar da talauci, ta hanyar daukar takamaiman matakai, wadanda aka iya tabbatar da amfaninsu. (Bello Wang)