logo

HAUSA

Hukumomin MDD na ci gaba da kai agajin jin kai Niger

2023-08-15 09:32:35 CMG Hausa

Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da kai kayayyakin agaji Jamhuriyar Niger, makonni 3 bayan tsare zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum da masu tsaronsa suka yi.

Kakakin MDD Stephane Dujarric ya shaidawa manema labarai jiya a birnin New York na Amurka cewa, hukumomin na ci gaba da kai wa ga jama’a duk da kalubalen da ake fuskanta, ciki har da yanayi na damina.

Ya ce kimanin mutane miliyan 4.3 a kasar dake yammacin Afrika ne suka dogara da tallafin jin kai. (Fa’iza Mustapha)