logo

HAUSA

Sojojin ruwan Morocco sun ceto bakin haure 130 ‘yan kasar Senegal

2023-08-14 09:52:13 CMG Hausa

A jiya Lahadi ne kamfanin dillancin labaran MAP ya rawaito cewa, sojojin ruwan Morocco sun ceto ‘yan ci rani ‘yan kasar Senegal 130 a gabar tekun Atlantika kusa da birnin Dhakla.

Rahoton ya kara da cewa, wasu jami'an tsaron ruwa na kasar Morocco ne suka tare jirgin a lokacin da ya taso daga tashar ruwa ta Fass Boye da ke kasar Senegal a arewa zuwa tsibirin Canary na kasar Spaniya a tekun Atlantika.

Har ila yau, a ranar Lahadin, tsibirin Canary ya ba da sanarwar cewa, jami'an cetonsu sun kama wani kwale-kwalen tare da ceto mutane 53 da ke cikin jirgin a gabar tekun Fuerteventura.

An samu karuwar shigowar bakin haure 'yan Afirka ta hanyar kwale-kwale zuwa tsibirin Canary na kasar Spaniya a cikin watan Agusta saboda kyawun yanayi. (Yahaya)