logo

HAUSA

An bukaci ’yan sandan Najeriya da su rinka amfani da dabarun zamani wajen gudanar da aikinsu

2023-08-13 15:20:35 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya hori jami’an ’yan sandan kasar da su rinka kula da ka’idojin aiki tare kuma da amfani da sabbin dabarun zamani da duniya ke amfani da shi wajen gudanar da aikinsu.

Shugaban ya yi wannan kira ne jiya Asabar 12 ga wata yayin bikin yaye daliban kwalejin horas da jami’an ’yan sanda dake Wudil a jihar Kano ta arewacin Najeriya.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. //////

 

Bayan gabatar da farati na musamman da dalibai 169 da aka yaye suka gudanar, shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Sanata Kashim Shettima ya ce, yanzu tsarin tsaro a duniya ya sauya kamar yadda ’yan ta’adda suka sauya matakan da suke bi wajen aiwatar da ayyukan ta’addanci, a sabo da haka akwai bukatar ma’aikatan tsaro su kara fadada tunani da kuma kwarewarsu.

Sanata Kashim Shettima ya ce, yanzu Najeriya na bukatar zakwakuran matasa masu jinni a jiki wadanda suke da hangen nesa da kaifin tunani a bangarorin tsaron kasa.

Mataimakin shugaban kasar ta Najeriya ya sake jaddada kudirin gwamnatin tarayyar Najeriya na ci gaba da taimakawa kwalejin a matsayinta na fitacciyya wajen bayar da horo a kan sha’anin tsaro ba kawai a Najeriya ba har ma a kasashen Afrika dake yammacin Sahara.

“Ina tabbatar muku da irin kokarin da gwamati ke yi na samar muku da damarmakin da za ku ji dadin hidimtawa kasa, sai dai kalubalen a nan shi ne sai lallai an samar da kwararrun jami’ai da aka horas a bangaren gudanarwar aiki da mu’amulla ta zamantakewa tare da cusa da’a, kishin kasa da kuma himma. Na gamsu sosai da irin horon da kuka samu a tsawon shekaru 5 da kuka yi a kwalejin, na tabbatar kuma a shirye kuke ku hidimtawa wannan kasa.” (Garba Abdulahi Bagwai)