logo

HAUSA

Kamfanin gine gine na CITIC ya mika sashen karshe na aikin ginin babbar hanyar mota a Aljeriya

2023-08-13 16:48:05 CMG Hausa

A jiya Asabar ne kamfanin gine gine na kasar Sin CITIC, ya mika sashen karshe na aikin ginin babbar hanyar mota da ta hade sassan larduna 17 dake kasar Aljeriya. Karkashin babban aikin ginin hanyar, CITIC ya kammala ginin kilomita 84 na hanyar.

Hanyar wadda ta hade sassan gabashi da yammacin kasar, ta dangana daga birnin Drean na lardin El Tarf a gabas mai nisa, zuwa birnin Raml Souk mai iyaka da kasar Tunisiya.

Yayin bikin kaddamar da sashen karshe na wannan katafaren aiki a birnin  El Tarf, firaministan Aljeriya Aymen Benabderrahmane, ya jinjinawa muhimmin matsayin wannan aiki, wanda ya ce zai saukaka zirga zirgar matafiya, ta bunkasa hada hadar tattalin arziki tsakanin al’ummun Aljeriya da na Tunisiya.

Benabderrahmane, ya kuma yabi ingancin aikin hanyar, yana mai cewa, injiniyoyin kasar Aljeriya, da ‘yan kwadago da suka shiga aka dama da su a aikin, sun samu karin kwarewa da sanin makamar aiki.

Yayin bikin kaddamarwar, mataimakin babban manajan kamfanin CITIC a kasar Aljeriya Qi Shujie, ya ce injiniyoyin kasar Sin sun fuskanci manyan kalubale yayin da suke gudanar da aikin, ciki har da bukatar gudanar da ciko mai tarin yawa, da matsalar zaftarewar kasa, tun fara aikin ginin kilomita 84n a shekar 2017, amma duk da haka, sun kai ga kammala aikin a kan lokaci.

Kaza lika, wata sanarwa da kamfanin na CITIC ya fitar, ta ce kamfanin ya sauke nauyin dake wuyan sa, yayin da yake gudanar da ginin hanyar, wanda ya kunshi kafa cibiyar jagoranci, da ta lura da nagartar aiki, kana ya horas da dubban ma’aikatan hanya na kasar ta Aljeriya.  

Har ila yau, kamfanin ya gudanar da ayyukan tallafawa al’ummun dake makwaftaka da aikin, ciki har da shiga ayyukan bunkasa jin dadin jama’a, kamar bayar da tallafi ga iyalai mabukata yayin azumin watan Ramadan, da gina filayen dakile yaduwar gobar daji, da samar da daukin ambaliyar ruwa.   (Saminu Alhassan)