logo

HAUSA

ECOWAS ta ba da umarnin samar da dakarun kota kwana da za su maido da demokradiyya a Nijar

2023-08-11 10:29:10 CMG Hausa

Kungiyar raya tattalin kasashen yammacin Afrika ta bayar da umarnin samar da dakarun kota kwana da za su dawo da mulkin demokradiyya a jamhuriyyar Nijar.

A yayin da yake karanta jawabin bayan taron kolin da kungiyar ta gudanar jiya Alhamis, 10 ga wata a birnin Abuja, fadar gwamnatin tarayyar Najeriya, shugaban hukumar gudanarwar kungiyar Omar Alieu Touray ya ce, wannan hukunci shi ne mafita da zai kai ga cimma burin kungiyar na tabbatar da sahihin mulkin demokradiyya a kasar ta Nijar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Kafin shugaban hukumar gudanarwa ta kungiyar ta ECOWAS ya kai ga karanta jawabin bayan taron, sai da shugaban kungiyar kuma shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya shaidawa shugabanni membobin kungiyar da suka halarci taron cewa, “domin mu nuna sadaukar da kanmu ga demokradiyya da kare hakkin dan adam, da kuma kyautatuwar rayuwar al’ummar Nijar, ya sanya tun farko muka fara amfani da tsarin tattaunawa ta diplomasiyya da sojin da suka kitsa juyin mulkin.”

A lokacin da yake karanta jawabin bayan taron ga manema labarai, shugaban hukumar gudanarwar kungiyar ta ECOWAS Omar Alieu Touray ya ce, taron ya sake yin alawadai da ci gaba da tsare shugaba Mohamed Bazoum da iyalansa.

Daga bisani Omar Alie Touray ya lasafto matakai na gaba da taron kungiyar ta ECOWAS ya amince da dauka a kan haramtacciyar gwamnatin sojin Nijar tare da kira ga kungiyar tarayyar Afrika da MDD da sauran kawayen kasashe da kuma hukumomin kasa da kasa da su goyi bayan sabbin matakan.

Wasu daga cikin sabbin matakan matsin lambar dai sun hada da.

“Baiwa dakarun sojin kasashen Ecowas umarnin shirin ko ta kwana domin maido da tsarin mulkin farar hula a Nijar. Kara jaddada tare da amfani da dukkannin matakan da suke kunshe cikin taron gaggawa da aka gudanar a kan kasar ta Nijar a ranar 30 ga watan jiya wadanda suka hada da haramcin tafiye-tafiye da rufe iyakokin kasar da kuma kwace kaddarorin mutanen da suka aiwatar da juyin mulkin.”

Haka kuma taron ya ja kunnen wasu kasashe mambobin kungiyar da suke kokarin kawo cikas ga samun nasarar tsare-tsaren kungiyar ta Ecowas na wanzar da zaman lafiya a kasar ta Nijar. (Garba Abdullahi Bagwai)