logo

HAUSA

Birnin Jinhua na kara kyautata alaka da kasashen Afirka

2023-08-11 15:05:39 CMG Hausa

A shekarar 2022, darajar hada hadar shige da fice ta birnin Jinhua na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, ta kai kudin kasar yuan biliyan 683.87, adadin da ya karu da kusan ninki 54, idan an kwatanta da na shekarar 2002. Cikin wannan adadi, darajar hada hadar fitar da hajoji ta birnin ta kai matsayi na 7 tsakanin dukkanin biranen kasar, kana saurin karuwar darajar hada hadar shigo da hajoji ta birnin ya kai matsayin farko tsakanin dukkanin biranen lardin Zhejiang. A dai shekarar ta 2022, hada hadar fitar da hajoji daga birnin Jinhua zuwa kasashen Afirka, ya kai kaso 33.3 bisa dari na daukacin hada hadar da aka yi a lardin Zhejiang a wannan fanni, kana ta kai kaso 8 bisa dari cikin jimillar na kasar Sin baki daya.

Wani salon zance da ake yi cewa, "Alkiblar hadin gwiwar Sin da Afirka ta karkata ga lardin Zhejiang, kana alkiblar hadin gwiwar Zhejiang da Afirka ta karkata ga birnin Jinhua", yana kara samun matukar karbuwa.  (Saminu Alhassan)