logo

HAUSA

Madam Guichen Aghaichata Atta mace mafi karancin shekaru a cikin sabuwar gwamnatin Nijar

2023-08-11 10:41:08 CMG Hausa

Daga cikin ministoci 21 na sabuwar gwamnatin faramanista, Ali Mahamane Lamine Zeine domin rikon kwarya da aka kafa a rana jiya alhamis 10 ga watan Augustan shekarar 2023. Nada mace mai shekara 28 da aifuwa ya kasance abin alfahari ga matasan Nijar.

Abin da ya dauki hankalin ‘yan Nijar musammun ma matasa maza da mata shi ne nada a ma’aikatar kula da aikin hannu da yawon bude ido wata matashiyar mace, wacce kuma ita ce mace ta farko mafi karancin shekaru a tarihin kasar Nijar har ma a nahiyar Afrika da ta rike wannan kujera.

Ganin cewa kasar Nijar kasa ce ta al’adun gargajiya inda ayyukan hannu suke taka muhimmiyar rawa cikin rayuwar al’umma, domin haka ne sana’ar aikin hannu ta zama abin runguma daga wajen maza har zuwa mata, kuma kabilun Nijar musammun ma Abzinawa sun kasance mutanen da suka fi shahara wajen aikin hannu da kuma suka fi rike al’adun gargajiya na aikin fata da aikin karfe. Haka a Nijar, bangaren yawon bude ido na da muhimmancin gaske, ganin cewa shekaru da dama wasu yankunan Nijar misalin yankin Agadez ko yankin Tillabery har ma zuwa yankin Diffa sun kasance wuraren yawon bude ido ga mutanen kasashen yammacin duniya da ma shiyyar asiya inda kowace shekara, mutane daga wadannan kasashe suke zuwa a Nijar.

Aikin hannu da yawon bude ido na da muhimmancin gaske ga cigaban tattalin arziki da jama’a. Dalilin haka ne, aka nada madam Guichen Aghaichata Atta mai shekaru 28 da haifuwa sabuwar ministar aikin hannu da yawon bude ido, wanda hakan ya ja hankalin ’yan Nijar ganin cewa, madam Aghaichata, mace ce da ta dukufa da nacewa wajen bunkasa da baiwa al’adun gargajiya darajarsu da kuma tana nuna kokarinta cikin harkokin kyautatuwar jin dadin matasa. Haka zalika Aghaichata mamba ce ta kungiyar agaji ta Scout-Niger, kuma ta yi karatun jami’a inda ta samu digirin master 2 a fannin ’yancin harkoki a kasar Morroco.

’Yan Nijar da dama suke sa ran, madam Guichen Aghaichata Atta za ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa da raya ayyukan hannu da yawon bude ido domin kara haskaka tutar Nijar a idon ’yan Nijar da ma duniya. Daga karshe, kasancewarta minista mafi karancin shekaru a cikin gwamnatin rikon kwarya a Nijar na baiwa matasan Nijar musamman ma mata kwarin gwiwa wajen neman a dama da su cikin harkokin ci gaban kasa. (Maman Ada)