logo

HAUSA

An gudanr da taron hadadden kwamitin kula da tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afrika ta Kudu

2023-08-11 14:19:42 CMG Hausa

Ministan kula da harkokin cinikayya na kasar Sin Wang Wentao da takwaransa na Afrika ta Kudu Ebrahim Patel, sun jagoranci taro karo na 8 na hadadden kwamitin kula da cinikayya da tattalin arziki na kasashen biyu a Pretoria dake kasar Afrika ta Kudu. Ministocin sun kuma yi musayar ra’ayi kan zurfafa dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashensu, tare da share fagen taron shugabannin kungiyar BRICS karo na 15 a fannonin cinikayya da tattalin arziki.

Wang Wentao, ya ce a shirye Sin take a dama da ita yadda ya kamata a sabon shirin zuba jari na Afrika ta Kudu da fadada jarinta a bangaren sabon makamashi da kere-kere da hakar ma’adinai da aikin gona da sauran fannoni, tare kuma da hada gwiwa a bangarorin ayyukan masana’antu da tsarin samar da kayayyaki.

Ya ce yana fatan Afrika ta Kudu za ta samar da yanayi mai kyau tare da bayar da goyon baya ga kamfanonin kasar Sin kamar na kayayyakin laturoni da na ababen hawa da sauransu, domin su gudanar da harkokinsu a kasar.

A nasa bangare, Ebrahim Patel ya ce Afrika ta Kudu na daukar Sin a matsayin abokiyar huldar cinikayya da tattalin arziki mafi muhimmanci, haka kuma tana matukar yabawa kyakkywar rawar da kamfanonin Sin ke takawa wajen raya zamantakewa da tattalin arzikin kasarsa.

Ya ce Afrika ta Kudu za ta ci gaba da kyautata muhallinta na kasuwaci tare da maraba da kamfanonin kasar Sin domin amfani da sabuwar damarmakin da yankin cinikayya mara shinge na nahiyar Afrika ya kawo, da nufin gudanar da karin hadin gwiwa a fannonin cinikayya da tattalin arziki a kasar. (Fa’iza Mustapha)